Siyasa

Muhimman abubuwa biyar game da samun man fetur a Arewacin Najeriya

A wannan ranar Talata shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Gombe da Bauchi.

A cikin shekarar 2019 ne dai kamfanin mai na ƙasar wato NNPC ya bayyana gano tarin arzikin albarkatun man fetur a yankin na Kolmani a kan iyakar Bauchi da Gombe da ke yankin arewamaso gabas a Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yankin Kolmani na da arzikin albarkatun man fetur da ya kai ganga biliyan ɗaya da kuma kyubik biliyan 500 na iskar gas a cikin kasa.

Shugaban ƙasar ya faɗa a wajen taron cewa an samu masu zuba waɗanda suka zuba jarin da ya kai dala biliyan uku da dori domin aikin haƙo man na Kolmani.

Ga wasu jerin alfanu da masana suka ce za asamu sakamakon wannan aiki:
Alfanu ga Najeriya
Dokar kashi 13 cikin dari
Dokar PIA
Rage gorin da ake yi wa Arewa kan fetur
Samun aikin yi ga ‘yan yankin
Kasancewa aikin yanada buƙatar ƙwararru, kuma duk da cewa babu wata doka da ta ce dole sai an ɗauki ‘yan yankin aikin a masana’antar, amma dole idan ‘yan yankin suna da ƙwararru da sukafi cancanta su samu aiki, to za su iya samu, kamar yadda Dakta Ahmed ya ce.
Sannan akwai ayyukan ƙarfi zallah kamar gini da ƙananan ayyukan gadi da irinsu leburanci to wannan mutanen yankin duk su za su samu wannan, hakan kuma zai sa su samu kuɗin shiga.

”Haka kuma watakila idan nan gaba aka samu sauyi game da kundin tsarin dokoki da mulki inda ake cewa jihohi su mallaki albarkatun da ke yankunsu, to ga ka johohin za su ci ribar wannan sosai da sosai,” in ji Dakta Ahmed.

Sai dai duk da wannan alfanu akwai wasu ƙalubale da ke tattare da man wannan aiki, waɗanda suka hadar da gurɓacewar muhalli ta hanyar gurɓata musu ƙasar noma da haddasa musu hayaƙi da zai guɓata musu muhalli uwa uba.

Related Articles

Back to top button